Kungiyar Izala ta yi Allah wadai da kisan gillar da 'yan kabilar Birom suka yi wa Musulmai

Kungiyar Izala ta yi Allah wadai da kisan gillar da 'yan kabilar Birom suka yi wa Musulmai

Shugaban kungiyar Izala Sheikh Abdullahi Bala Lau, yayi Allah wadai da tare hanya da 'Yan Kabilar Birom a jihar plateau suka yi suna zakulo musulmai da Hausawa suna musu kisan Gilla a jiya Lahadi.

Jaridar Premium Times tace an kashe matafiya sama da 120 Ciki harda wasu 'yan agajin Izala mazauna garin Mangu Ustaz Zhahradden Sufi da Ustaz Sha'aban kasuwan Ali

A wani rahoto ance motoci da dama wadanda suke bi ta Baifas musamman wasu kauyuka anan jihar plateau domin saukin shiga Jos, daga Abuja lamarin ya auka musu.

Kungiyar Izala ta yi Allah wadai da kisan gillar da 'yan kabilar Birom suka yi wa Musulmai
Kungiyar Izala ta yi Allah wadai da kisan gillar da 'yan kabilar Birom suka yi wa Musulmai

Shugaban Izala Sheikh Abdullahi Bala Lau, yayi kira ga gwamnatin tarayya data gaggauta zakulo masu hanu a wannan ta'addanci a hukuntasu, ba daidai bane kullum a zura musu ido suna kashe bayin Allah wadanda basuji ba ba su gani ba.

KU KARANTA KUMA: Kauracewa babban taron APC da Kwankwaso yayi alamu na cewa harkar siyasarsa ya zo karshe – Garba

Adalci shine gwamnati tabi kadun wadanda aka kashe.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng