Ainihin dalilin da yasa Babangida ya hana Abiola mulki - Sule Lamido

Ainihin dalilin da yasa Babangida ya hana Abiola mulki - Sule Lamido

- Sule Lamido ya bayyana dalilin da ya sa gwamnatin soja ta rsa zaben 1993

- Tsohon gwamnan ya ce gwamnatin sojan ta yi tunanin marigayi Cif MKO Abiola zai yi amfani da mulki wajen karban kudin da yake bin ta

- Game da cewa Lamido, Abiola na bin gwamnatin Babangida N45 billion na ayyukan kwangila da yayi musu ta hanyar ma;aikatar sadarwa

Tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma tsohon sakataren jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), Sule Lamido, ya ce marigayi Cif Moshood Abiola na bin hukumar sojin Najeriya bashin kudi N45 billion kafin rasuwarsa.

Lamido yace wannan bashi da yake binsu na ayyukan kwangila ne da yayi wa ma’aikatar sadarwan Najeriya a lokacin.

Ainihin dalilin da yasa Babangida ya hana Abiola mulki - Sule Lamido
Ainihin dalilin da yasa Babangida ya hana Abiola mulki - Sule Lamido

Jaridar Punch ta bada rahoton cewa Alhaji Sule Lamido yayinda yake tsakoci kan abinda ya faru aka rusa zaben June 12, yace tunda ya bayyana cewa Abiola ne zai lashe zaben kuma har yanzu bata biyashi bashin da yake binta ba.

KU KARANTA: Dalilin da yasa bamu halarci taron APC ba - Kwankwaso

Yace: “Lokacin da Murtala Mohammed ya rasu, Abiola ya yi ikirarin cewa yana bin gwamnatin kudi, ina ganin N45 billion na ma’aikatar sadarwa.

Shugabannin soji a lokacin suka ce sam basu yarda ba. Sai ya bi sarakunan Arewa domin su sanya baki kuma sarakunan suka cewa soji su taimaka su biya kudin.

Soji suka ce sun rusa zaben June 12 ne saboda idan suka bari ya zama shugaban kasa, zai dauki kudinsa kuma kasa za ta talauce.”

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng