Cin fuska ko yabawa: An baiwa dalibin da ya zamo zakara a jami’a kyautar Naira dubu biyu

Cin fuska ko yabawa: An baiwa dalibin da ya zamo zakara a jami’a kyautar Naira dubu biyu

- Maganar da ake yawaita yi kan cewa ilimi shi ne mafita na neman zamowa wasan yara, duba da yadda ake yiwa waɗanda suka nunawa bajintarsu rashin muhimmanci

- Wata jami'a ta yiwa wani dalibi kyautar dubu biyu bayan fita da sakamako mafi kyau

Har kullum idan mutane musamman manya suka ta shi magana ka ilimi sai ka ji su suna cewa ilimi shi ne mafita, amma bisa dalilin sauyawar zamani da yawan mutane na ganin ya kamata kodai ayi gyara a harkar ilimin ko kuma su masu faɗin waccan maganar su daina.

Sau tari zaka ji yadda ake yabawa duk wani wanda yayi kokarin azo a gani da fatar baki amma babu wani batun ihsani ko kyautar da zata sanya ɗalibin sake dagewa don nuna bajintarsa.

Amma kuma abu ne mai mutuƙar sauki a baiwa waɗansu mutane kyautar da ta shalle hankali bisa wata bajintar da suka nuna.

KU KARANTA: Tun a duniya: Jami'ar OAU ta kori Farfesan da ya nemi kwanciya da ɗaliba don ya bata maki

Misalin irin wannan kamaceceniya shi ne, kyautar Naira 2,000 kacal da aka baiwa wani ɗalibi da yayi babar bajintar kammala karatunsa da takarda sakamako mafi kololuwar bajinta ta Distinction a jami'ar jihar Ekiti.

Cin fuska ko yabawa: An baiwa dalibin da ya zamo zakara a jami’a kyautar Naira dubu biyo
Cin fuska ko yabawa: An baiwa dalibin da ya zamo zakara a jami’a kyautar Naira dubu biyo

Amma kuma aka baiwa waɗansu matasan da suke shirin TV na BB Naija kyautar miliyoyin kuɗi har ma ta kai ga gwamnonin jiharsu sun ƙara musu da kyautar Motar hawa da wasu kyautukan. Duk kuwa da sukar da ake yiwa shirin saboda baɗalar da ake aikatawa a cikinsa.

Cin fuska ko yabawa: An baiwa dalibin da ya zamo zakara a jami’a kyautar Naira dubu biyo
Cin fuska ko yabawa: An baiwa dalibin da ya zamo zakara a jami’a kyautar Naira dubu biyo

Yayin da shi kuma ɗalibin da ya shafe shekaru yana wahalar karatu aka ba shi kyautar dubu biyu.

To abin tambayar a nan shi ne, shin anya kuwa da gaske a halin yanzu ilimi shi ne mafita?

Amsar na da wahalar gaske amma dai mutukar aka cigaba a haka to tabbas matasa zasu dawo daga rakiyar damuwa sai sunyi karatu, sannan su mayar da hankalinsu kan yin abin shiriritar da yake janyo hankalin mutane sannan ya kawo musu kuɗi.

Dafatan mahukunta zasu zage damtse wajen yabawa duk ɗaliban da suka nuna hazaƙa ta hanyar yi musu kyautuka masu gwaɓi don nuna jin daɗi da kuma ƙara musu kwarin gwuiwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng