Shugaba Buhari ya aika sakon ta’aziyarsa ga iyalan marigayi Sarkin Fadan Kano

Shugaba Buhari ya aika sakon ta’aziyarsa ga iyalan marigayi Sarkin Fadan Kano

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon ta’aziyarsa ga iyalan marigayi Sarkin Fadan Kano, Sule Gaya, wanda ya rigamu gidan gaskiya a jiya Alhamis, 21 ga watan Yuni, 2018.

Shugaba Buhari ya ce rasuwan Sule Gaya babban rashi ne ga Najeriya saboda mutum ne mai matuka tawali’u, gaskiya, tsoron Allah da kuma jajircewa.

Buhari ya siffanta Sarkin Fadan Kano a matsayin abin alfahari ga iyalinsa da jiharsa, ya ce Sule Gaya ya sadaukar da shekaru 107 da yayi a doron kasa wajen rayuwa mai albarka da bautawa kasa.

KU KARANTA: Hukumar yan sanda ta damke yan yankan kai 3

A matsayinsa na tsohin dan majalisan dokokin Arewa kuma tsohon ministan kananan hukumomi a jamhurriya na biyu, shugaba Buhari ya ce Sule Gaya na cikin yan siyasan da suka yi gwamnati da mutunci da gaskiya.

Shugaba Buhari ya ce babban addu’an da yaransa za su yi shine kwaikwaiyan halin kan-kan da kai, gaskiya da bautan kasa da yayi a rayuwarsa.

A karshe, Buhari ya mika sakon ta’aziyyarsa ga masarautar Kano, gwamnatin jihar da mutanen jihar Kano.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel