Kasafin kudin Buhari, ba na kasa baki daya ba ne, na kasar Yarbawa ne - Shugaban Kungiyar cigaban matasan Arewa

Kasafin kudin Buhari, ba na kasa baki daya ba ne, na kasar Yarbawa ne - Shugaban Kungiyar cigaban matasan Arewa

Kamar yadda kuka sani ana cigaba da cece-kuce akan kasafin kudin 2018 wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu akai a ranar Laraba, 21 ga watan Yuni.

Yayinda wasu suke ganin aibun matakin da majalisar dokoki ta dauka na yin ragi ga kudaden da shugaban kasar ya gabatar masu, bah aka abun yake ba a bangaren kungiyar cigaban matasan Arewa.

Domin shugaban kungiyar, ya zargi gwamnatin Buhari da mayar da hankali wajen gina kudancin kasar da raya jama'ar su musanman yankin Yarbawa, yayin da yankin arewa ya zamo koma baya an ci yaki dashi sannan an barshi da kuturun Bawa

Kasafin kudin Buhari, ba na kasa baki daya ba ne, na kasar Yarbawa ne - Shugaban Kungiyar cigaban matasan Arewa
Kasafin kudin Buhari, ba na kasa baki daya ba ne, na kasar Yarbawa ne - Shugaban Kungiyar cigaban matasan Arewa

Shugaban Kungiyar Gambo Ibrahim Gujungu ya bayyana hakan, lokacin da yake zantawa da manema labarai a kaduna dangane da batun kasafin kudin shekarar 2018 da shugaban kasa ya sanyawa hannu.

KU KARANTA KUMA: Cikin manyan yan siyasa da na yan kwangila ya duri ruwa bayan EFCC sun yi barazanar ziyartan ayyukan NDDC da aka yasar

Gambo Gujungu ya cigaba da cewar abin takaici ne da bakin ciki yadda Buhari yayi wa yankin Arewa butulci duk da gudummuwar da jama'ar yankin suka ba shi wajen yi mishi ruwan kuri'u wanda ya kai ga lashe zabe, amma abin mamaki sai gashi a kasafin kudin bana kuma kasafi na karshe a mulkin Buhari, sama da kashi 95 na ayyukan raya kasa an tattara su a yankin kudancin Nijeriya, an bar yankin Arewa cikin kangi da talauci gami da koma baya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng