Cikin manyan yan siyasa da na yan kwangila ya duri ruwa bayan EFCC sun yi barazanar ziyartan ayyukan NDDC da aka yasar
Ibrahim Magu, mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rasahawa (EFCC), ya gabatar da jan kunne ga yan kwangila da suka yasar da ayyukan miliyoyin naira a fadin Niger Delta.
Yace zai yiwa wajen dirar mikiya a ko wani lokaci domin duba matakin aikin da akayi zuwa yanzu domin kwatantawa da irin kudin da aka biya su, jaridar Vanguard ta ruwaito.
Magu yayi wannan jan kunne ne a ranar Alhamis, 21 ga watan Yuni.
Magu ya bayyana cewa duk inda kudaden gwamnati ya shiga ba tare da anyi ayykan da ya kamata bat oh duk wadanda ke da hannu ciki zasu fuskanci shari’a.
Mukaddashin shugaban na EFCC yayi Magana ne a Abuja lokacin da jami’an kungiyar daliban Niger Delta (NANDS) suka kai masa ziyara.
KU KARANTA KUMA: Kasafin 2018: Da shugaba Buhari ya sani bai sanya hannu akai ba – Sanata Shehu Sani
ya bayyana cewa akwai bukatar hukumar yaki da rashawa ta ziyarci yankin sannan ta tabbatar da cewar kudaden da aka biya don ayyukan cigaba amma akaki yi sun dawo sannan a hukunta wadanda suka taka doka.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng