Yanzu Yanzu: Hukumar DSS ta kama tsohon gwamnan jihar Benue, Suswam

Yanzu Yanzu: Hukumar DSS ta kama tsohon gwamnan jihar Benue, Suswam

Jami’an yan sandan farin kasa wato DSS sun kama tsohon gwamnan jihar Benue, Mista Gabriel Suswam, kan lamuran tsaro a jihar.

An kama tsohon gwamnan ne bayan gwamna mai ci, Mista Samuel Ortom ya aika wasika ga hukumar DSS kan lamarin tsaro a jihar inda ake zargin Suswam da shirin lalata gwamnatin.

Wata majiya kusa da gwamnan wadda ta nemi a boye sunanta ta tabbatar da kamun da kuma wasikar ga majiyarmu ta Channels TV a ranar Alhamis.

Yanzu Yanzu: Hukumar DSS ta kama tsohon gwamnan jihar Benue, Suswam
Yanzu Yanzu: Hukumar DSS ta kama tsohon gwamnan jihar Benue, Suswam

Dss ta taba kama tsohon gwamnan a 2017, bayan an gano muggan makamai daga wasu kayayyaki da ake zargin nasa ne a gida mai lamba 44 Aguiyi Ironsi way, Maitama Abuja.

KU KARANTA KUMA: 2019: Matasan Kudu sun amince da Buhari ya sake takara

Idan baza ku manta ba a samu tashe-tashen hankula a yankin Benue sakamakon kashe-kashen da ake zargin makiyaya da kaiwa jama'a a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel