Gwamnatin Buhari tayi shirin aiwatar da titin jirgin kasa da zai zagaye jahohi 9 da Abuja – Amaechi

Gwamnatin Buhari tayi shirin aiwatar da titin jirgin kasa da zai zagaye jahohi 9 da Abuja – Amaechi

- Hankali gwamnatin tarayya na shirin sada jahohin kasar nan da layin dogo

- Da zarar an cimma yarjejeniyar cin bashin wani sashin biyan kudin aiwatar da ginin titin za'a fara aikinsa

- Wannan karon ma dai kasar China da Exim Bank ne zasu bayar da bashin

Ministan sufuri na kasa Chibuike Rotumi Amaechi ya bayyana cewa gwamnatin tarayya tayi shirin aiwatar da gina titunan jirgin kasa da zai zagaya cikin jahohi 9 na yammacin kasar nan da kuma birnin tarayya Abuja wanda jimillar tsayinsa zai kai nisan kilomita 1,402Km.

Gwamnatin Buhari tayi shirin aiwatar da titin jirgin kasa da zai zagaye jahohi 9 da Abuja – Amaechi
Gwamnatin Buhari tayi shirin aiwatar da titin jirgin kasa da zai zagaye jahohi 9 da Abuja – Amaechi

Amaechi ya zayyana hakan ne yayin gabatar da jawabinsa jiya Laraba a wurin taron da aka gudanar a birnin Beijing na kasar China da akaiwa lakabi da ‘Kyakkyawan hanyar sufuri ita ce kyakkyawar duniya’.

Ministan ya bayyana cewa aikin za’a kammala shi ne cikin watanni 36 da zarar an cimma yarjejeniyar aron kudin da za’a gudanar da aikin tsakanin gwamnatin Najeriya da China.

KU KARANTA: An damke ƴan ƙasashen ƙetare 300 a wurin rijistar katin zabe

Enter headlineMaximum length: 150a kuma zai kai kimanin kilomita 1,402Km, sannan za’a kammala aikin shi ne a cikin shekaru uku idan har an kammala yarjejeniya da wadanda zasu biya wani sashi domin aiwatar da aikin da suka hada da EXIM Bank kamar yadda ake sanya rai”. A cewar Amaechi.

Kan maganar ginin layin dogo na Lagos zuwa Kano da aka bawa kamfanin China Civil Engineering and Construction Company (CCECC), wanda kasar China da EXIM Bank shi ma zasu biya wani sashe ne gudanar da aikin, Amaechi ya shaida cewa bayan kammala aikin zai kasance hanyar sada madatsar shigo da kaya kasar nan ta ruwa zuwa kan tudu na Arewacin Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng