An tare manyan hanyoyi a jihar Kaduna yayinda za’a gurfanar El-Zakzaky yau
An rufe manyan hanyoyin zuwa babban kotun jihar Kaduna da safiyar yau Alhamis, 21 ga watan Yuni yayinda ake shirin gurfanar da shugaban kungiyar IMN da aka fi sani da Shi’a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.
Yan jaridan da suka tafi kotun basu samu daman shiga ba yayinda manyan jami’an tsaro suka tare dukkan hanyoyi domin hana jama’a samun isa harabar kotun.
Hakazalika masu abubuwan hawa basu saman daman wucewa ba daga Kabala doki zuwa Indepence way zuwa Waff road.
Kana daliban kwalegin kimiya da fasaha na Kaduna wato Kadpoly basu samu daman isa makaranta ba.
Mun kawo muku rahoton cewa yan kungiyar Shi’a sun samu sabani da jami’an yan sandan yayin wani zanga-zanga da suka yi a titin Ahmadu Bello way a jiya Laraba, 20 ga watan Yuni.
Sheikh Ibrahim El-Zakzaky dai yana gurfana a kotu ne kan laifin tara mabiya ba bisa doka ba, kokarin fito-na-fito da gwamnati.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng