Ni ma dan Tijjaniyya ne - Inji Shugaba Buhari

Ni ma dan Tijjaniyya ne - Inji Shugaba Buhari

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa shi fa na kowane dan Najeriya ne mai irin kowane addini, yare ko kabila ciki kuwa hadda Tijjaniyya tare da cewa shi babban burin sa shine na samar wa da 'yan kasa cigaba mai dorewa.

Shugaban yayi wannan ikirarin ne a fadar sa dake a Villa, jiya lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin darikar Tijjaniya a nahiyar Afrika karkashin jagorancin Sheikh Ahmed Tijjani Ibrahim Inyass dake zaman jika wurin Marigayi Sheikh Ibrahim Inyass.

Ni ma dan Tijjaniyya ne - Inji Shugaba Buhari
Ni ma dan Tijjaniyya ne - Inji Shugaba Buhari

KU KARANTA: Damfara: EFCC ta fitar da sabuwar sanarwa

Legit.ng ta samu cewa Buhari ya godewa dukkan 'yan tijjaniyya dake a fadin duniya game da irin goyon bayan da suke nuna masa da kuma fahimtar manufofin sa na alheri da suke yi.

A wani labarin kuma, Shugaban kungiyar Kiristoci a Najeriya watau Christian Association of Nigeria, CAN mai suna Samson Ayokunle ya nesanta kungiyar sa da wani rahoto da suka ce yana yawo na cewa suna goyon bayan takarar tazarcen shugaba Buhari a zaben 2018.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Fasto Adebayo Olajide, mataimakin sa na musamman akan harkokin watsa labarai da ya ce su kungiyar su ba ta siyasa bace.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel