Mahaukaciyar iska tayi barna a Kazaure gidajen mutane da yawa sun lalace

Mahaukaciyar iska tayi barna a Kazaure gidajen mutane da yawa sun lalace

- Mutane sun shiga matsala a Kazaure a dalilin lalata musu gidaje da iska tayi

- Kwanan rufin gidaje da kuma jijiyoyin bishiyoyi ne suka zazzare a yayin da garin ya fuskanci iskar mai karfin gaske mai kama da guguwa

Sama da gidaje 200 suka lalace a garin Kazaure na jihar Jigawa sakamakon wata iska mai karfin gaske.

Wannan na fitowa ne daga bakin shugaban hukumar bayar da tallafin gaggawa na kasa shiyyar jihar jigawa reshen karamar hukumar ta Kazaure Malam Sale Nuhu.

Mahaukaciyar iska tayi barna a Kazaure gidajen mutane da yawa sun lalace
Mahaukaciyar iska tayi barna a Kazaure gidajen mutane da yawa sun lalace

Amma sai dai ya bayyana cewa har yanzu suna cigaba da lissafa wadanda ta’adin iskar ya shafa, sai ya zuwa lokacin magana da majiyarmu sun lissafa gidaje sama da dari biyu da abin ya shafa.

Lamarin da ya faru a ranar Asabar an dai rawaito ya garin ya fuskanci matsananciyar iskar da ta haddasa rushewar gidaje da kuma faduwar bishiyoyi.

KU KARANTA: Gwamanatin tarayya zata gina wuraren kiwo 94 a jahohi 10

Wani mazaunin yankin da abin ya faru mai suna Bala Idi, ya lissafa sama da gidaje 100 da abin ya lalata tun bayan da aka fara iskar da misalin karfe 6:00pm na yamma, inda ya bayyana mafi yawancin gidajen da abin ya shafa sun fuskanci dayewar kwanan rufin gidajensu yayin da jijiyoyin bishiyu kuma suka zazzare.

Idi ya kuma kara da cewa karfin iskar ya sanya mutanen yankin shiga cikin halin dimuwa da ifacce-iface.

Shi ma wani mazaunin yankin Babangida Andu ya ce, iskar ta cefa yankin nasu a duhu sakamakon tsittsinke wayoyin wutar lantarkinsu da ta yi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel