Da kudin barayi Buhari yaci zaben 2015 - Inji PDP

Da kudin barayi Buhari yaci zaben 2015 - Inji PDP

- Jam'iyyar PDP a Najeriya ta yi wa Shugaba Buhari wanjin babban bargo

- Jam'iyyar dai ta bayyana cewa da kudin barayi Buhari yaci zaben sa na 2015

- PDP ta ce in da gaske ne to ya binciki yadda ya samu kudin

Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya ta PDP ta bayyana cewa shugaban kasar Najeriya baya da wata kima ko kwarjinin da zai zo yana ta faffaka game da yaki da cin hanci da rashawa idan dai har bai binciki inda kudaden kamfe din sa na 2015 suka fito ba.

Da kudin barayi Buhari yaci zaben 2015 - Inji PDP
Da kudin barayi Buhari yaci zaben 2015 - Inji PDP

KU KARANTA: An kara samun 'yar takarar shugaban kasa a 2019

Wannan kalamin dai sun fito ne daga ofishin babban sakataren yada labarai na jam'iyyar ta PDP Kola Olagbondiyan a yayin wani taron jam'iyyar a jihar Kogi.

Legit.ng ta samu cewa Mista Kola ya ce abun takaici ne yadda shugaban ke fitowa yana ta kumfan baki game da yaki da cin hanci da rashawa amma kuma a dayan bagaren yana zagaye da barayi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSAK KU:: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel