Cikin ƙasashe 5 na Africa Senegal ce kaɗai ta fidda su kunya
- Daga karshe daya cikin biyar ta yi rawar gani a gasar kofin Duniya
- Senegal ce kasar farko daga Africa da ta samu nasarar wasanta na farko
A ƙarshe dai an samu ƙasa ɗaya tilo daga cikin ƙasashe 5 da suka wakilci Nahiyar Africa a gasar cin kofin Duniya da ake gudanarwa a ƙasar Rasha.
Senegal ta samu nasara kan takwararta ta kasar Poland da ci 2-1 a daren yau.
Murnan wannan nasara tabbas ba zata tsaya ga ƴan wasan kasar ta Senegal dake can ƙasar rashan ba, ko mutanen babban birnin ƙasar Dakar ba, sai dai murnar zata zagaya duk nahiyar Africa musamaman a zuƙatan masoya kwallon ƙafa.
Ƙasashen Africa guda 4 Egypt, Morocco, Nigeria da kuma Tunisia duk sun sunyi rashin nasara a hannun takwarorinsu a wasanninsu na farko.
KU KARANTA: Yadda wata yarinya ‘yan shekara 12 da ta ceci rayukan mutane 300 a Zimbabwe
Haka Senegal ta sanya ƙasar ta shiga fili domin taka leda gwuiwarta a sanyaye ganin sauran takwarorinta na Africa 4 duk sun sha kashinsu a hannu har da uwa mabada mama Najeriya.
Ashe wani abu da ba'a sani ba shi ne sun fito ne da fushi domin ɗaukar fansa.
Ɗan wasan Senegal Idrissa Gueye ne ya fara zura kwallo a ragar ƙasar Poland kafin tafiya hutun rabin lokaci
Sannan sai Mbaye Niang ya zura kwallo ta biyu a mintuna 61. Kafin dan wasan kasar Poland Krychoviak ya farke kwallo guda a minti na 86 ta hanyar jefa kwallon da kansa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng