An yankewa iyaye masu shayarwa 3 da wasu mutane biyu daurin watanni shida gidan yari kan laifin satar kaji na kimanin N3.2m

An yankewa iyaye masu shayarwa 3 da wasu mutane biyu daurin watanni shida gidan yari kan laifin satar kaji na kimanin N3.2m

Wata kotun Majistare dake Osogbo ta tura wasu iyaye masu shayarwa uku da aka ambaci sunayensu a matsayin Regina Phillip (40), Cecilia Ochili (25), Elizabeth Ankara da kuma wasu maza biyu Odebiyi Yinka (20) da Ayoola Samson, gidan yari.

Kotun ta yanke musu hukunci a ranar Talata kan laifin satar kaji da suka kai kimanin naira miliyan 3.2.

Dan sanda mai kara, Inspekta Adegoke Taiwo ya sanar da kotun cewa masu laifin biyar sun hada kai wajen aikata laifin a ranar 5 ga watan Yuni, a Erin Osun, dake Osogbo, jihar Osun.

Yayi bayanin cewa Odebiyi Yinka da Ayoola Samson sun sace kaji 1,600 da farashin su ya kai naira miliyan 3.2 mallakar gonar Misis Aluko Titilayo dake Erin Osun, inda ya kara da cewa matan uku ne suka amshi kajin daga hannunsu, alhalin sun san na sata ne.

An yankewa iyaye masu shayarwa 3 da wasu mutane biyu daurin watanni shida gidan yari kan laifin satar kaji na kimanin N3.2m
An yankewa iyaye masu shayarwa 3 da wasu mutane biyu daurin watanni shida gidan yari kan laifin satar kaji na kimanin N3.2m
Asali: UGC

Lauyan dake kare masu laifin ta roki kotu da tayi adalci da rangwame, inda tace masu laifin sunyi nasarar biyan wacce ke kara N200,000 yayinda da ta roki ayi duba ga masu shayarwan.

KU KARANTA KUMA: Jerin sunaye: Tsoffin gwamnonin Najeriya shida da aka yankewa hukunci bayan kama su da laifin aikata rashawa

Da take yanke hukunci, jagorar kotun Awodele Modupe Adedoyin ta yankewa masu laifin watanni shida agidan yari tare da biyan N10,000 ko wannensu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng