Yadda wata yarinya ‘yan shekara 12 da ta ceci rayukan mutane 300 a Zimbabwe

Yadda wata yarinya ‘yan shekara 12 da ta ceci rayukan mutane 300 a Zimbabwe

- Yarinya karama ‘yar shekara 12 tayi wani aikin bajinta na ceton mutane da yawa

- Yarinyar ta sanar da samun matsala a layin dogon kasar Zimbabwe, wanda hakan ya taimaka wajen Dakar da jirgin

- Mutane da dukiya mai yawa ce dai aka ceto sakamakon bayanan da ta bayar

An jinjinawa wata yarinya mai shekaru 12 bisa bajintar da ta nuna na kai rahoto ga hukumomin tsahar jiragen kasa na kasar Zimbabwe kan matsalar da titin jirgin ya samu.

‘Yar baiwa: Kalli hoton yarinya ‘yan shekara 13 da ta ceci rayukan muatane 300 a Zimbabwe
‘Yar baiwa: Kalli hoton yarinya ‘yan shekara 13 da ta ceci rayukan muatane 300 a Zimbabwe

Yarinyar da aka bayyana sunanta da Nozipho Sibanda wadda take a ajin farko a karamar makarantar sakandire ta Entumbane High School, ta kai rahotan ne bayan da ta gano cewa layin dogon ya karye ta wani bangare a yankin Sawmills a watan Satumba.

Kai wannan rahotan ne ya sanya aka yi maza aka dakatar da tashin jirgin wanda yake shirin kwasar har mutane 300. Wannan bajinta ce ta sanya aka bata lambar girmamawa ta hukumar jiragen kasa ta kasar.

KU KARANTA: Kowa ya hau motar kwaɗayi: Kotu ta yankewa wasu ƴan uwa biyu hukuncin wata 6 a dadlin satar TV plasma

Hukumar jiragen kasan ta kasar ta kuma je har can makarantar su yarinyar domin shaidawa makarantar irin namijin kokarin da tayi, sannan kuma suka biya mata kudin makarantarta har ta gama.

Sannan kuma hukumar jiragen kasar ta kasar ta shaida cewa zata tanadar mata gurbi a ma’aikatarta mutukar tana sha’awar zama ma’aikaciya idan ta gama makaranta, kamar yadda jami’in shiyya Joseph Temai na hukumar jiragen kasan kasar ya shaida.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng