Gudun dukan mahaifiyarta ya sanya wata yarinya zabar shan gubar da ta kaita har lahira

Gudun dukan mahaifiyarta ya sanya wata yarinya zabar shan gubar da ta kaita har lahira

- Tsoron hukuncin mahaifiya ya sanya wata yarinya shekawa barzahu

- Amma sai dai hukuncin da ta dauka yafi zarce kima, domin yayi sandiyyar mutuwarta

- 'Yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin

A jiya ne a jihar Legas aka tabbatar da rasuwar wata yarinyar yar shekaru 15 da haihuwa, Rukayat Taiwo ta rasu ne ta hanyar shan guba domin gujewa duka daga mahaifiyarta.

Ya zuwa yanzu dai ba a bayyana laifin da yarinyar ta aikata ba, amma jaridar vanguard ta rawaito cewa yarinyar ta gudu daga gida ne bayan da mahaifiyar tace sai ta zane ta bisa laifin da tayi mata, yarinyar ta gudu daga gidan ne saboda kar a dake ta a ranar Lahadi tun da safe kuma ba ta dawo ba sai da daddare idan daga nan ne ta yi ta korafin cikin ta na mata ciwo.

Gudun dukan mahaifiyarta ya sanya wata yarinya zabar shan gubar da ta kaita har lahira
Gudun dukan mahaifiyarta ya sanya wata yarinya zabar shan gubar da ta kaita har lahira

Nan take dai aka garzaya da ita asibitin Agatha daga bisani kuma aka sake kai ta babban asibitin Ighanmu wanda a nan ne ta bayyana cewa ta sha gubar ne don gudun kar mahaifiyarta ta doke ta.

KU KARANTA: Yan Boko Haram sun saki sabon bidiyonsu a dajin Sambisa

Bayan da majiyarmu ta kai ziyarar gani ga ido domin samun bayani game da abinda ya faru a gidan su yarinyar dake lamba 31 Adeez Hgoro a Jakande, a yankin Okokomaiko na Jihar Legas.

Wani mazaunin yankin mai suna Jimoh ya bayyanawa manema labarai cewa "Dukkan mu abin ya bamu mamaki saboda ranar lahadi da safe tana cikin yara 'yan uwanta tana wasa amma da yamma sai naji wasu suna cewa sun ganta da kwalbar gubar a hannunta amma babu wanda ya yi tsammanin ta sha wannan gubar".

A yayin da take kan gadon asibiti ta bayyanawa mahaifiyarta da sauran mutanen dake wajen cewa ta sha gubar ne da zummar gujewa dukan da mahaifiyarta tace zata yi mata ne amma bata san cewa abinda ta sha yana haɗari ga rayuwarta ba, wanda hakan ya yi sanadiyyar zama ajalinta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng