Yan Boko Haram sun saki sabon bidiyonsu a dajin Sambisa
- Bidiyon da 'yan Boko haram suka saki ya nuna cewa har yanzu da burbushinsu
- Bidiyon ya nuna yadda suke gudanar da Sallar idi bayan kammala Azumi
Cikin wani yanayi dake nuna cewar har yanzu suna nan daram, ƴan ƙungiyar Boko Haram sun saki wani sabon bidiyo dake nuna yadda suje gudanar da Sallar idi a fili a dajin Sambisa.
Bidiyon mai tsawon mintuna biyar da dakika 17 da wakilin kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya gani a Maiduguri, ya nuna ƴan ta'addan suna sanye da kayan Sallarsu tare da iyalansu suna gabatar da Sallar idi bayan kammala Azumi 29 na watan Ramadan.
Bidiyon dai an hakikance cewa an dauke shi ne a danin Sambisa wurin da ake ganin nan ne babban sansanin ƴan ta'addan a jihar Borno inda suka fi ƙarfi.
KU KARANTA: Abin ya zo: Laftanar janar Buratai ya kaddamar da fadan karshe akan Boko Haram (Hotuna)
A cikin bidiyon an hasko wani guda da yaƙi bayyana kansa yana godiya ga Ubangiji bisa raya shi da yayi ya ga bikin Sallar.
"Muna son duniya ta san cewa muna nan a raye kuma muna cikin farin ciki da wannan rana".
Wani ma ɗan Boko Haram ɗin ya ce, yana cikin nishaɗi kuma ya ƙra da cewa "A jira a gani bala'o'i na nan tafe"
Sai dai a cikin bidiyon babu shugabansu Abubakar Shekau kwata-kwata duk kuwa da cewa ana kyautata zaton gungun na ƴan tsagensa ne.
A kwanan baya ne dai rundunar sojin Najeriya ta ƙaddamarda wani atisaye mai taken fadan ƙarshe domin gamawa da ƴan ta'addan baki ɗaya a yakin tafkin Chadi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng