Wata sabuwa: An bukaci hukumar ICPC ta binciki jagoran majalisar wakilan Najeriya

Wata sabuwa: An bukaci hukumar ICPC ta binciki jagoran majalisar wakilan Najeriya

- Kungiyar HEDA ta bukaci hukumar nan dake yaki da almundahana ta kasa ta binciki Honorable Gbajabiamila

- HEDA tace sayen motar Naira miliyan 78 da yayi akwai lauje cikin nadi

- Haka ma sun ce siyen motar da yayi yana nuna bai damu da talakawa

Wata kungiya mai rajin tabbatar da demokradiyya da mulki mai adalci mai suna Human and Environmental Development Agenda (HEDA) a turance ta bukaci hukumar nan ta gwamnatin tarayya ta ICPC da ta soma bincikar Femi Gbajabiamila, dan majalisa mai wakiltar mazabar Surulere.

Wata sabuwa: An bukaci hukumar ICPC ta binciki jagoran majalisar wakilan Najeriya
Wata sabuwa: An bukaci hukumar ICPC ta binciki jagoran majalisar wakilan Najeriya

KU KARANTA: Wutar cikin gida na shirin kone APC kurmus

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da suka fitar a ranar Litinin din da ta gabata inda suka nuna tsananin fushin su game da yadda dan majalisar ya fitar da zunzurutun kudade har Naira miliyan 78 domin siyen motar da ya ba matar sa kyauta a ranar zagayowar haihuwatar.

Legit.ng ta samu cewa takardar koken da kungiyar ta HEDA ta kaiwa hukumar ta ICPC na dauke ne da sa hannun shugaban ta mai suna Olanrewaju Suraju.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng