Zaben kananan hukumomi: Jam'iyyar PDP tayi wa APC zigidir a wannan jihar

Zaben kananan hukumomi: Jam'iyyar PDP tayi wa APC zigidir a wannan jihar

Kamar dai yadda muka samu, babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya kuma mai mulki a jihar Ribas ta lashe dukkan zabukan kananan hukumomin da aka gudanar a jihar a karshen satin da ya gabata da babban rinjaye da hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar ta gudanar.

Shugaban hukumar zaben na jihar, Mai shari'a Chukwunenye Uriri dai shine ya sanar da sakamakon zabukan a garin Fatakwal, babban birnin jihar inda ya kuma bayyana cewa an gudanar da zaben ne cikin lumana da kwanciyar hankali.

Zaben kananan hukumomi: Jam'iyyar PDP tayi wa APC zigidir a wannan jihar
Zaben kananan hukumomi: Jam'iyyar PDP tayi wa APC zigidir a wannan jihar

KU KARANTA: Sabon harin kunar bakin wake ya halaka mutum 31 a Borno

Legit.ng ta samu cewa haka zalika shugaban hukumar zaben ya godewa daukacin 'yan jihar game da yadda suka fito sosai suka gudanar da zabukan nas.

A wani labarin kuma, Wata kungiya mai rajin tabbatar da demokradiyya da mulki mai adalci mai suna Human and Environmental Development Agenda (HEDA) a turance ta bukaci hukumar nan ta gwamnatin tarayya ta ICPC da ta soma bincikar Femi Gbajabiamila, dan majalisa mai wakiltar mazabar Surulere.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da suka fitar a ranar Litinin din da ta gabata inda suka nuna tsananin fushin su game da yadda dan majalisar ya fitar da zunzurutun kudade har Naira miliyan 78 domin siyen motar da ya ba matar sa kyauta a ranar zagayowar haihuwatar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel