Rundunar sojin sama tura jirage 2 jihar Zamfara domin su yi maganin ta’addanci

Rundunar sojin sama tura jirage 2 jihar Zamfara domin su yi maganin ta’addanci

Rundunar sojin sama na Najeriya ta aika da jirage masu saukar ungulu biyu ga sansanin 207 Quick Response Group Air Force Base dake Jihar Zamfara domin magance matsalar tsaro da yan ta’adda.

An tura jiragen ne domin taimakawa jami’an dake yaki da barayin shanu da sauran yan ta’adda a jihar.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa kwanan nan hukumar sojin sama ta kaddamar da filin saukar jirgi mai tashi da saukar ungulu a sansanin Quick Response Air Force Base dake Gusau.

Rundunar sojin sama tura jirage 2 jihar Zamfara domin su yi maganin ta’addanci
Rundunar sojin sama tura jirage 2 jihar Zamfara domin su yi maganin ta’addanci

Jami’an da aka tura jihar sun hada da sojoji, yan sanda, yan sandan farin kaya, da sojin sama.

KU KARANTA KUMA: Kaduna 2019: Zan kara da El-Rufai – Shehu Sani

Da yake Magana a yayin karban jiragen, kwamandan kungiyar, Kyaftin Caleb Olayera ya bada tabbacin cewa jihar zata ga chanji.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel