Sanata yayi rabon N500 a matsayin rarar Dimokradiyya (hotuna)
A bayyane yake a daidai lokacin da zaben 2019 ke gabatowa, yan siyasa daban-daban na amfani da dabaru domin siye zukatan masu jefa kuri’u.
Don haka wani Sanata daga mazabar Ogun East kuma dan takarar gwamna a zaben 2019 Buruji Kashamu na irin nasa dabarar domin siye zukatan jama’a da kuma kafa sunansa.
Ya rarraba yar karamar kwali na shinkafa da kuma kudi naira dari biyar (500) ga mutanen mazabarsa.
Akwai hasashe cewa dan siyasan wanda ake nema a kasar Amurka bisa zargin safarar miyagun kwayoyi na iya sauya sheka zuwa wata jam’iyya nan bada jimawa ba domin ganin ya cimma mafarkinsa na zama gwamna a jihar Ogun.
Ga hotunan kasa:
KU KARANTA KUMA: Dan shekara 22 ya yiwa mahaifiyarsa duka har lahira saboda ta ki amincewa da soyayyarsa da kanwarta
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng