Wani matashi ya sake kashe kansa a masallacin Makkah (Hotuna)
- Wani matashi ya sake kashe kansa a masallacin Makkah
- Mamacin ya jefo kan sa ne daga ginin hawa na farko
- Wanda ya kashe kan sa din ya fadowa wani dan kasar Sudan
A karo na biyu cikin kwanaki bakwai kacal, an kara samun wani matashin daga kasar Bangladesh da ya sake kashe kan sa a masallaci mai alfarma na garin Makka a cikin satin da ya gabata kamar dai yadda muka samu.
KU KARANTA: Wutar cikin gida na shirin kone APC kurmus
Kamar dai yadda muka samu daga majiyar mu, mamacin ya jefo kan sa ne daga ginin hawa na farko na masallacin Ka'aban inda ake dawafi yayin da mutane ke cike a wurin suna ta yin ibada.
Legit.ng ta samu cewa wanda ya kashe kan sa din ya fadowa wani dan kasar Sudan ne mai shekaru sama da hamsin a duniya wanda hakan ya sa yaji munanan raunuka da yanzu haka ma yana asibiti yana karbar magani.
Mai karatu ma dai zai iya tuna cewa a farkon watan nan na Yuni lokacin azumi ma wani dan kasar Faransa ya kashe kansa a masallacin na makka.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng