Abin tausayi: Kalli Bidiyon yadda aka zaƙulo matar da Macijiya ta haɗiye
- Shirgegiyar Macijiya mai tsayin mita 23 ta kashe wata mata
- Bayan ta kashe ta sannan ta haɗiye ta baki ɗaya
- Amma ita bayan gano cewa ta haɗiye matar an farka cikinta
Abin mamaki da al'ajabi ya faru a ƙasar Indonesia, inda wata mesa ta haɗiye wata mata gaba ɗaya sannan ta haɗiye ta.
Wannan dai shi ne karo na biyu da a cikin shekara guda iron haka na faruwa a ƙasar. Matar mai shekaru 54 an dai bayyana sunanta da Wa-Tiba kuma har tana da ƴaƴa biyu.
An dai nemi matar ne an rasa tun bayan da ta je duba lambunta a lardin tsuburin Muna dake kudancin Sulawesi da yammacin ranar Alhamis.
Shugaban lardin Persiapan Lawela ne ya bayyana hakan. Da bata dawo ba har safiyar juma'a, sai yayarta ta fita nemanta amma kawai ta gano sahun takalminta da fitilarta da adda da kuma takalmanta.
KU KARANTA: Hotunan wata mata da aka gano a cikin wani katon maciji bayan kwanaki da bacewar ta Rashin ganin nata ne ya sanya ƴan uwanta da sauran mutanen lardin giye da 100 bazama nemanta. Bayan duddubawa kusa da inda aka ga sauran kayan nata ne aka hango wata shirgegiyar Macijiya mai tsayin mita 23 kusa da wurin.
Mesar bata ko iya motsa wanda hakan ya sanya su tunanin ko ta haɗiye matar, bayan kashe Macijiyar ne ƴan ƙauyen suka farka cikinta, kwatsam sai ga gawar Tiba a ciki. Kuma gawar cif take a cike ba tare da an raba ta ba, sanye da kayan cikinta, kuma kanta ne a karshen jelar mesar wanda hakan yake nuna cewa ta kai ta fara haɗiye ta.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng