Badakalar Naira miliyan 100: Su Rarara sun ba Gwamnan Zamfara Yari da El-Rufa'i hakuri

Badakalar Naira miliyan 100: Su Rarara sun ba Gwamnan Zamfara Yari da El-Rufa'i hakuri

Labarin da muka samu na nuni ne da cewa gungun fitattun mawakan nan na Hausa 'yan jama'iyyar APC watau All Progressives Congress (APC) Northern Musicians Forum (ANMFO) sun fito sun baiwa gwamnan Zamfara Abudul Aziz Yari da Gwamna El-rufai hakuri game da badakalar Naira miliyan 100 da ta taso a kungiyar tasu.

Kungiyar dai ta bayar da hakurin ne a cikin wata sanarwar sanarwar da ta fitar tare da gudanar da taron manema labarai da ta gudanar karkashin jagorancin mataimakin shugabanta Alhaji Murtala Mamsa Jos a garin Jos.

Badakalar Naira miliyan 100: Su Rarara sun ba Gwamnan Zamfara Yari da El-Rufa'i hakuri
Badakalar Naira miliyan 100: Su Rarara sun ba Gwamnan Zamfara Yari da El-Rufa'i hakuri

KU KARANTA: Babban dalili na na cewa Buhari yayi murabus - Gumi

Legit.ng ta samu cewa da a kwanan baya ne labari ya rika yawo na cewa daya daga cikin 'ya'yan kungiyar kuma fitaccen mawakin nan na Shugaba Muhammadu Buhari watau Dauda Kahutu Rarara ya yi sama da fadi da kudin kungiyar har Naira miliyan 100.

Sai dai 'yan kungiyar sun yi zargin cewa wasu makiya shugaba Buhari ne da kuma jam'iyyar ta su ta APC ke kokarin bata masu suna.

Haka zalika kungiyar ta bayyana cewa zargin badakalar bai da wani tushe balle makama.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng