Sabuwar PDP: Su Saraki, Baraje da Kwankwaso sun tattauna makomar su a Saudiyya

Sabuwar PDP: Su Saraki, Baraje da Kwankwaso sun tattauna makomar su a Saudiyya

Yayin da lokacin da aka sanya domin gudanar da babban taron gangamin jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ke ta kara karatowa, 'yan sabuwar jam'iyyar adawa ta PDP da suka koma jam'iyyar a gabanin zabukan 2015 na kara shiga duhu.

Sai dai kamar yadda majiyar mu ta bankado mana, wasu jiga-jigan 'yan siyasar da suka jagoranci 'yan sabuwar PDP din ya zuwa APC sun yi ta gudanar da tarukan sirri a kasar Saudiyya domin lalubo mafitar su.

Sabuwar PDP: Su Saraki, Baraje da Kwankwaso sun tattauna makomar su a Saudiyya
Sabuwar PDP: Su Saraki, Baraje da Kwankwaso sun tattauna makomar su a Saudiyya

KU KARANTA: An bukaci Buhari ya tsige shugaban INEC

Legit.ng ta samu cewa shugaban bangaren na 'yan sabuwar PDP din Kawu Baraje da kuma shugaban majalisar tarayya Sanata Bukola Saraki a musamman sun hadu a wajen Umarah inda kuma suka tattauna game da makomar tasu.

Kawo yanzu dai basu ce komai ba amma dai sun tabbatar ma majiyar mu da cewa a sati mai zuwa ne za suyi taro da sauran 'yan tafiyar tasu idan suka dawo Najeriya za kuma su sanar da mafita.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng