Hotuna: Shugaba Buhari ya halarci Sallar Idi a Abuja
-Shugaba Buhari ya yi Sallar bana a Abuja
-Gabanin yanzu, shugaban ya kasance yana cin bukin Salla a gida Daura
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci Sallar Idi a masallacin Mambilla Barracks da ke babban birnin tarayya Abuja sannan ya karbi bakuncin yan yawon Sallah a fadar shugaban kasa ta Aso Villa.
Daga cikin wadanda suka kawo masa ziyarar yawon Sallah sune gwamnan babban bankin tarayya, Mr Godwin Emefiele; sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustafa; ministan birnin tarayya, Muhammad Musa Bello; ministan tsaro, Mansur Dan Ali; ministan harkokin cikin gida, AbdurRahman Dambazzau.
Kana shugaba Buhari ya karbi bakuncin kananan yara da suka kawo masa ziyarar yawon Sallah.
Sauran sune Sanata mai wakiltan Abuja, Philip Tanimu Aduda; Sanata Bala Ibn Na'Allah, dan majalisa, Zakari Angulu Dobi; babban mai baiwa shugaban kasa shawara kan majalisar dattawa, Ita Enang.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng