Kilu ta ja bau: Wasu ƴan mata sun lakaɗawa samarin da za suyi musu fyaɗe duka, sannan suka miƙa su ga ƴan sanda

Kilu ta ja bau: Wasu ƴan mata sun lakaɗawa samarin da za suyi musu fyaɗe duka, sannan suka miƙa su ga ƴan sanda

- Garin neman gira wasu samari sun sara ido

- Yunkurin yiwa wasu 'yan mata fyade ya jefa wasu samari cikin matsala

- Bayan rashin nasara sun fada hannun 'yan sanda

Ƴan Indiyan dai sun kasance suna fakon ƴan Najeriyar mata guda biyu domin su yi musu fyaɗe. Amma sai dai reshe ya juye da mujiya domin kuwa yunƙurin ƴan Indiyan ya gaza cimma ruwa bisa ƙarfin tuwo da ƴan matan ke da shi. Ƴan matan suka murɗa mazan biyu sannan suka miƙawa jami'an ƴan sanda.

Kilu ta ja bau: Wasu ƴan mata sun lakaɗawa samarin da za suyi musu fyaɗe duka, sannan suka miƙa su ga ƴan sanda
Kilu ta ja bau: Wasu ƴan mata sun lakaɗawa samarin da za suyi musu fyaɗe duka, sannan suka miƙa su ga ƴan sanda

Jaridar Indian Times ta rawaito cewa, ƴan matan biyu suna tafiya domin komawa gidan da suke haya a garin Channai ranar Talata da daddare sai mazan suka hango su, nan take suka ga tamkar banza ta faɗi, kawai sai suka nufe su.

KU KARANTA: Satar Man Fetur ta jefa wasu 'Yan Najeriya 3 da 'Yan Kasar Ghana 2 a Gidan Wakafi

A zatonsu ƴan matan zasu gudu ko su tsorata, amma sai suma su kai kansu aka fara fafatawa. Ba a ɗauki wani dogon lokaci ba ƴan matan Najeriyar dake karatunsu a ƙasar ta Indiya suka nannaushe su, da samarin suka ji matsa sai suka fara neman taimako.

Daga ƙasrshe suka miƙa su ga jami'an ƴan sanda, sannan ne aka gane ashe a make su mankas da barasa.

Jami'an ƴan sanda sun bayyana cewa guda daga cikin ƴan matan na karatu ne a makarantar Loyola College yayin da ɗayar take a Madras Christian College.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel