Muhimman batutuwa 5 game da Ali Al-Mulla - shugaban masu kiran sallah a masallacin Makkah
Ko shakka babu muryar Ali Ahmed al-Mullah shugaban ladanai kuma babban mai kiran sallah a masallacin makka ta karade dukkan lungu da sako na duniyar musulmai domin irin zakin da take da ita.
Kamar dai yadda muka samu a hadissan Manzon tsira, Muhammadu S. A. W, kiran sallah na da matukar lada sannan kuma masu yin sa ma suna da matukar falala a cikin al'ummar musulmi duniyar su da lahira.
KU KARANTA: An ga wata a Saudiyya, gobe sallah
Legit.ng ta tattaro mana wasu muhimman batutuwa biyar da game da mai kiran sallah a masallacin makka da yafi kowa dadewa a tarihin masallacin.
1. Ali Ahmed al-Mullah gadon kiran sallah yayi daga mahaifin sa
2. Ana yi masa nakabi da sunan Bilal
3. An haifi Ali Ahmed al-Mullah a shekarar 1945
4. Ya fara kiran sallah a masallacin makka tun yana da shekaru 14 a duniya
5. An nada shi a matsayin mai kiran sallah a masallacin Makka a hukumance a shekarar 1975.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng