Ya kamata Buhari ya ba iyalan Yar’adua da sauransu hakuri – Shehu Sani

Ya kamata Buhari ya ba iyalan Yar’adua da sauransu hakuri – Shehu Sani

Sanata Shehu Sani mai wakiltan yankin Kaduna ta tsakiya a majalisar dokokin kasa yace ya kamata shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba iyalan marigaji Janar Shehu Musa Yar’adua, Dr Beko Kuti, Chima Ubani, da na Ken Saror Wiwa hakuri.

Shehu Sani ya bayyana hakan ne a shafinsa na twitter a ranar, Alhamis, 14 ga watan Yuli.

Shugaban kasar a madadin gwamnatin tarayya ya baiwa iyalan marigayi Abiola wanda ya lashe zaben 1993 hakuri.

Ya kamata Buhari ya ba iyalan Yar’adua da sauransu hakuri – Shehu Sani
Ya kamata Buhari ya ba iyalan Yar’adua da sauransu hakuri – Shehu Sani

Sani ya wallafa a shafinsa cewa: “Akwai bukatar gwamnatin tarayya ta baiwa iyalan Ken Saror Wiwa da mutansa na Ogoni hakuri sannan ta karrama su.

KU KARANTA KUMA: Labari mai dadi: Marigayiya Hauwa Maina ta samu jika

“Sannan kuma ta aikata hakan ga marigayi janar Shehu Musa Yar’adua. Sannan kuma ya zama dole a tuna da Dr. Beko Kuti da Chima Ubani”.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin samun ingantattun labarai ku bide mu a

Facebbook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel