Bacin rai yasa wata mata ta watsawa mijinta ruwan zafi
- Tsautsayi ko ganganci ya sanya wata zubawa mijinta ruwan zafi
- Yanzu haka dai dangin mijin sun maka ta a kotu
- Tana can ido yayi wiki-wiki
A yau Alhamis ne wata kotun majistiri dake zamanta a Ikeja ta tuhumi wata mata mai shekaru 32 da haihuwa mai suna Joy Imeribe da laifin watsawa mijinta ruwan zafi.
Ɗan Sanda mai gabatar da ƙara Clifford Ogu ya bayyana kotun cewa, wadda ake tuhumar ta dawo gida ne a kurarren lokaci wanda hakan yasa maigidan nata Ibe ya tambayi ba'asin hakan shi ne ta fusata.
Mai shigar da karar yace shi ne washegarin ranar da safe yana cikin karin kumallo ta watsa masa ruwan zafi a jikinsa, wanda hakan ya jawo ya samu munanan raunuka, amma nan take maƙwabtansa suka garzaya dashi asibiti. Ma'auratan sun dade da aure har sun kai shekaru 13 kuma suna da yara guda hudu.
KU KARAN: Motar ‘yan sanda tayi karo da ta sojoji a Abuja
Iyalan mai gidan ne dai suka nuna rashin amincewarsu bisa wannan rashin imani da kuma ɗiban albarka. suka shigar da kara a caji-ofis din 'yan sanda kuma nan take aka cafke ta tare da gurfanar da ita gaban kotun.
Laifin dai ya saɓawa kundin manyan laifuka ƙarƙashin sashin na 245 na Jihar Legas na shekara ta 2015. Kotun ta gindaya sharuda domin bada belin wadda ake tuhumar akan kudi har Naira dubu 100,000 tare da kawo mutane biyu da zasu tsaya mata kafin bayar da belinta.
Daga nan ne kuma kotun ta ɗage zaman har sai 4 ga watan Yulin da za a shiga.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng