Kotu ta aika sammaci ga shugaban DSS na Kano cewa ya gurfana gabanta a ranar 13 ga watan Yuli
Wata babban kotun jihar Kano ta umurci darakta na hukumar yan sandan DSS reshen jihar Kano da ya gurfana a gabanta a ranar 13 ga watan Yuli kan sanya baki da kawo tsaiko ga wani lamarin dake gabanta ba bisa doka ba.
Shugaban kotun, Mai shari’a Lawan Adamu, ya kuma umurci Barista Dalhatu Shehu Usman da wani Auwalu Buhari da sun gurfana gabanta kan dalili guda.
An basu umurnin ne domin su samu damar yin bayani kan dalilin da yasa jami’in DSS ya shiga wani lamari game da mallakar wani shago a Kantin-Kwari.
Shari’an ya kasance tsakanin Alhaji Ibrahim Talle mai kara da Hajiya Rakiya Sa’idu amatasayin mai karewa.
KU KARANTA KUMA: Shari’an Nyame da Dariye ya nuna cewa bama son kai - EFCC
Da farko kotun ta umurci daraktan DSS da wasu biyu su gurfana gabanta amma Barista Usman kadai ne ya gabatar da kansa a kotu a jiya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Za ku iya samun mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng