Rikicin makiyaya da manoma ya sake zama sanadin mutuwar mutane 4 da raunata da yawan gaske

Rikicin makiyaya da manoma ya sake zama sanadin mutuwar mutane 4 da raunata da yawan gaske

- Barkewar sabon rikicin manoma da makiyaya ya bar baya da kura a jihar Nassarawa

- Mutane hudu sun mutu wasu da yawa sun ji rauni yayin da 2 suka bace

- 'Yan kabilat Tiv sunyi kira da a kai musu dauki

A kalla mutane hude ne ‘yan kabilar Tiv suka bakunci lahira a wani rikici da ya afku ranar Talatar da ta gabata tsakanin wasu da ake zargin makiyaya ne a kauyen Gada-Biu dake karamar hukumar Obi ta jihar Nassarawa.

Sannan kuma wasu mutane 2 Aondovihi Tuur da Virlumun Atsaga an neme su an rasa, sanann kuma wasu kimanin 20 suka sami raunika daban-daban.

Rikicin makiyaya da manoma a jihar Nassarawa ya sake zama sanadin mutuwar mutane 4 da raunata da yawan gaske
Rikicin makiyaya da manoma a jihar Nassarawa ya sake zama sanadin mutuwar mutane 4 da raunata da yawan gaske

Hatsaniyar ta afku ne kimanin sati biyu kacal da cimma yarjejeniyar mayar da takubba cikin kube tsakanin ‘yan kabilar ta Tiv da kuma kungiyar makiyaya a jihar.

Wani wanda abin ya faru a idonsa mai suna Dennis Utsa, ya shaidawa jaridar Nigerian Tribune cewa, kashe-kashen ya afku ne da misalin karfe 10:00am na safe yayin da iyalan duka ‘yan gida daya ke kan hanyarsu ta zuwa gona.

KU KARANTA: Mutum 1 ya rasa ransa, an cafke 2 a wani rikici da ya barke a kaduna

Utsa ya ce, “Maganar da ake yanzu haka jami’an tsaro sun nufi wurin da abin ya faru domin zuwa taho da gawarwakinsu daga gonar da aka kashe su zuwa garin Kadarko”. Sannan ya bayyana sunayen wadanda suka mutun da; Utindi Kyor da Shie-Aondo da Dedzugwen, da kuma Boyi.

Da yake magana da ‘yan jaridu kan dawowar mummunar aika-aikar makiyayan, shugaban kungiyar kabilar Tiv a jihar Thomas Gar, ya bayyana cewa iyalan su hudu an kashe su ne yayin tafiyarsu gona.

Sannan ya kuma kara da cewa, tun bayan zuwan mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, yayi alkawarin aikowa da jami’an tsaro domin magance matsalar amma har yanzu shiru ba wani labara, wanda hakan ya kara sanya rikicin kara kamari a jihar.

“Har yanzu mutanenmu na sansanin ‘yan gudun hijira domin neman mafaka ba tare da sun koma gida ba, ga shi kuma damuna na kara yin nisa” Thomas ya bayyana cikin korafi.

A dalilin haka ne yayi kira ga mahukunta da su kara zage damtse wajen kokarin magance rikicin a sakamakon ‘yan kabilar ta Tiv suna cikin mawuyacin hali a jihar.

Amma da majiyarmu ta tuntubi kakakin hukumar ‘yan sanda ta jihar ta Nassarawa ASP. Samaila Usman cewa yayi, har ya zuwa lokacin bai samun labarin faruwar lamarin ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng