Shari’an Nyame da Dariye ya nuna cewa bama son kai - EFCC

Shari’an Nyame da Dariye ya nuna cewa bama son kai - EFCC

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa wato EFCC, tace hukunci da aka yanke kwanan nan ya nuna cewa bata nuna son kai kamar yadda wasu yan Najeriya ke zargi.

Legit.ng ta rahoto labarin tura tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame da tsohon gwamnan jihar Filato, Joshua Dariye gidan yari da akayi a ranar Talata.

An yanke wa ko wannenshu hukunci shekaru 14 ba tare da tara ba sakamakon wadaka da suka yi da kudaden jihohinsu a lokacin da suke mulki.

Dukkansu biyun sun ci zabe karkashin lemar PDP, sannan kuma aka sake zabarsu a 2003.

Shari’an Nyame da Dariye ya nuna cewa bama son kai - EFCC
Shari’an Nyame da Dariye ya nuna cewa bama son kai - EFCC

An fara shari’ansu ne tun a 2007 kafin a yanke musu hukunci bayan shekaru 11 a 2018.

KU KARANTA KUMA: An kama matashi dan shekara 18 dake shigar mata yana damfarar maza

A wata sanarwa da hukumar EFCC ta fitar a ranar Laraba ta bayyana cewa tura tsoffin gwamnonin biyu da akayi gidan yari da kuma shari’an da ake kan fafatawa a yanzu ya nuna cewa basa son kai don yin alfarma ga jam’iyya mai mulki wato APC.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Za ku iya samun mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng