Karshen aikin sojojin Najeriya 320 yazo amma ckin salama har da tagomashi

Karshen aikin sojojin Najeriya 320 yazo amma ckin salama har da tagomashi

- Na gwamna ga rawa ga yaki, soja marmari daga nesa

- Bayan kammala wa'adin aikinsu na hidimtawa kasa, yanzu haka an sanya ranar da wasu sojoji zasu ajiye aikinsu

- Amma kafin tube kakin nasu sai da aka horas da su sana'o'i da dabarun tattalin arziki

Adadin sojojin da za su ajiye aikinsu a mako mai zuwa ya kai 320 a cewar babban jami’in sojan sama Air Vice Marshal Austine Jekenu kwamandan cibiyar kula da sojojin da wa’adin aikinsu ya kammala (NAFRC).

Karshen aikin sojojin Najeriya 320 yazo amma ckin salama har da tagomashi
Karshen aikin sojojin Najeriya 320 yazo amma ckin salama har da tagomashi

Jekenu ya shaidawa manema labarai a cibiyar dake Oshodi a jihar Legas a yau Laraba, cewa sojojin masu shirin yin ritayar sun fito ne daga cikin rundunar sojojin ruwa da na kasa da kuma na sama.

A cewarsa 262 sojojin kasa ne sai da 44 kuma suke na ruwa, sai kuma 14 da suka kasance sojojin sama.

KU KARANTA: Sojin ruwan Najeriya sunyi fata-fata da matatun man fetur 1000 da aka gina ba bisa ka'ida ba

Kwamandan ya ce sojojin da suke shirin ajiye aikin sun shafe watanni a cibiyar suna karbar horo kan sana’o’i da dabarun kasuwanci domin kimtsa su gabanin fara sabuwar rayuwarsu bayan sun kammala aiki domin su taimaka wajen habaka tattalin arzikin kasar nan.

Daga nan ne kuma Jekenu yayi kira garesu da su yi cikakken amfani da wannan dama ta hanyar rike sana’o’in da zasu fara hannu biyu-biyu.

Ya zuwa yanzu dai cibiyar ta horas da tsoffin sojojin kasar nan da suka ajiye aiki har dubu 41, 000. Sannan ya kara da cewa bikin yaye sojojin masu ritaya na wannan lokaci za’a gudanar da shi ne ranar 22 ga watan Yuni kuma ministan tsaro Mansur Dan Ali zai halarta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng