Satar manja ta yi sandiyyar kwanan gidan yari ga wani saurayi
- Kuliya manta sabo inji masu iya magana
- Hakan kuwa ta faru da wani matashi da ya saci manjan wata mata
- Kotin ta ingiza keyarsa zuwa gidan yari har ya zuwa zamanta na gaba
Alkalin wata kotun majistire mai zamanta a Ado-Ekiti ta ingiza wani mutum mai suna Habibu Deribe zuwa gidan yari sakamakon satar manja wata mata mai suna Ramota Ibrahim da ya kai na Naira dubu N34, 000.
Wanda ake zargin mai shekaru 25 yanzu haka dai yana fuskantar tuhumar laifin haurawa da kuma sata a gidan mutane.
‘Dan sanda mai gabatar da kara Sufeto Johnson Okunade ya shaidawa kotun cewa, wanda ake zargin ya haura gidan mai karar ne da misalin karfe 2:00 a.m na dare, inda ya saci jarkar manjan a ranar 2 ga watan Yuni a Usi-Ekiti.
KU KARANTA: Kamarin talauci: Rashin kudin jarrabawar WAEC ya sanya wasu matasa fara fashi
A cewarsa wannan laifi ne da ya saba da sashi na 413(2) na kundin manyan laifuka na jihar da Ekiti 2012.
Sai tun kafin ayi maganar beli, ‘dan sandan ya soki lamirin duk wani yunkuri na yin hakan, domin a cewarsa kamata yayi a ingiza shi gidan maza har zuwa lokacin da za’a tuntubi shawarar ofishin daraktan lura da yanke hukunci (DPP).
Haka kuwa akai, domin mai shari’a Mr Adesoji Adegboye ya sanya a tisa keyar wanda ake zargin zuwa kurkuku, sanann ya dage zaman zuwa ranar 14 ga wata domin cigaba da sauraron karar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng