Yan bindigan Zamfara sun fara kai hari Sokoto, sun hallaka akalla mutane 13 – Kakakin hukumar yan sanda

Yan bindigan Zamfara sun fara kai hari Sokoto, sun hallaka akalla mutane 13 – Kakakin hukumar yan sanda

An yi artabu tsakanin yan banga da wasu yan bindiga a karamar hukumar Isa na jihar Sokoto inda akalla mutane 1 suka rasa rayukansu.

Wannan rikici ya faru ne bayan yan bindigan sukayi kokarin garkuwa da wani dattijo a kauyen dan tasango da ke Gebe ranan Juma’an da ya gabata amma basu samu nasara ba.

Dattijon ya nuna musu jan wuya kawai sai suka kashe shi. Wannan abu ya fusata yan banga gari wadanda suka fita neman yan bindigan.

Kawai sai sukayi arangama da su a hanyan Kamarawa-Bafarawa inda suka fara musayar wuta.

KU KARANTA: Daga karshe dai yau Buhari zai rattaba hannu kan kasafin kudin 2018

Game da cewar Idanuwan shaida, yan bindigan sun kashe yan banga 7 kuma yan banga sun samu nasaran kashe yan bindiga 5.

Kakakin hukumar yan sandan jihar Sokoto, DSP Cordelia Nwawe, wacce ta tabbatar da wannan hari ta ce mutane 8 aka rasa yan gari tare da dattijon.

Game da cewar ta, ana cigaba da gudanar da bincike domin damke yan bindigan kuma an gano yan bindigan jihar Zamfara ne suka shigo Sokoto.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel