Buhari ya karya Azuminsa tare da jakadun kasashen Duniya (Hotuna)
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakoncin jakadun kasashen Duniya daban daban a wata liyafar shan ruwa da ya shirya musu a fadar Villa a daren Talata, 12 ga watan Yuni, inji rahoton Legit.ng.
Wannan lifaya dai ta biyo bayan kammala taron karramawa da tunawa da yan gwagwarmayar Dimukradiyya, musamman a zaben shekarar 1993, da suka hada da Cif MKO Abiola da Babagana Kingibe daya gudana a fadar shugaban kasa da ranar Talata.
KU KARANTA: Kalla mutumin da Real Madrid ta nada a matsayin magajin Zidane
A wani labarin kuma, shugaba Buhari ya yi wata ganawar sirri da gwamnonin jam’iyyar APC a ofishinsa dake fadar Villa, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi zaben sabbin shuwagabannin jam’iyyar dake karatowa.
Ga dai wasu daga cikin hotunan shan ruwan da Buhari yayi sa jakadun kasashen Duniya.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng