‘Yan Najeriya na shirin darawa: Manyan Jiragen ruwa 6 sun iso Najeriya makare da kayan abinci da Fetir da Taki

‘Yan Najeriya na shirin darawa: Manyan Jiragen ruwa 6 sun iso Najeriya makare da kayan abinci da Fetir da Taki

- Maganganun mutane da yawa kan cewa gwamnatin tarayya na shirin shigowa da kayan abinci Najeriya na shirin zama gaskiya

- Yanzu haka labari daga majiya mai tushe da muka samu ya bayyana hakan a yau

- Tuni har jirage 6 sun iso yayin da ake cigaba da dakon karasowar wasu

Manyan jiragen ruwa shida makare da kayayyaki daban-daban ne suka iso gabar ruwan Najeriya ta jihar Legas.

‘Yan Najeriya na shirin darawa: Manyan Jiragen ruwa 6 sun iso Najeriya makare da kayan abinci da Fetir da Taki
‘Yan Najeriya na shirin darawa: Manyan Jiragen ruwa 6 sun iso Najeriya makare da kayan abinci da Fetir da Taki

Hukumar kula da shigowa da fidda kayayyaki ta ruwa (NPA) ce ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a yau Talata cewa, daga cikin kayan da jiragen ke dauke da su sun hada da; man fetir da madangantansa da takin noma da kuma kayan abinci.

KU KARANTA: Ana kashe kashe a Zamfara, Gwamna Yari yana tura mutane 5 kallon gasar cin kofin Duniya a Rasha

Haka zalika hukumar ta bayyana cewa tana da tsumayin sake samun shigowar wasu kayan da zasu shigo ta mashigar Apapa da kuma Tin-Can Island nan da ranar 12 zuwa 26 ga watan da muke ciki.

Su kuma jiragen da ake sa ran zuwan nasu suna dauke ne da Alkama mai tarin yawan gaske da daskararren Kifi da Tama da Karafa tare Dalma da Waken Soya da man Dizal da Sukari mai yan gaske da karin wani Takin Noman tare da man inji da sauransu. Kamar yadda NAN ya rawaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng