Jama’a sunyi cincirindo domin ganin gemun Manzon Allah a Turkiyya
Rahotanni da muka samu sun nuna cewa an fitar da gemun Annabi Muhammadu SAW daga wani babban masallaci mai daddeden tarihi a lokacin sahur domin mutane su gane ma idanunsu.
Kafar sadarwa ta TRT Hausa ta wallafa cewa a cikin masallacin Ulu dake garin Şanlıurfa ne aka fitar da gemun manzon tsira har guda 63 wadanda ake adane dasu tun shekaru masu tsawo da suka shige.
Dubban mutane sun yi tururuwa domin gane ma idanunsu gemun mai tsarki tare da yin kabbara da salati ga manzon tsira.
KU KARANTA KUMA: Masu haya 5 sun lalata yar mai gidansu mai shekaru 12 tare da yi mata ciki
An kuma ba mata damar zuwa ganin gemun har izuwa ranar Litinin, maza kuwa har izuwa ranar Lahadi.
A baya Legit.ng ta rahoto cewa wani babban malamin addinin Musulunci kuma limami a wani masallaci dake jihar Kano yayi gargadi kan yadda wasu mutane ka yiwa littafi mai tsarki rikon sakanar kashi harma wasu su taka bisa kuskure.
A cewar mallamin duk wanda ya wulakanta al-Qur'ani mai tsarki toh babu shakka ya kafurta.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin samun ingantattun labarai ku bide mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng