Kyal-kyal-banza: Wani dan Najeriya ya bizne mahaifin sa cikin motar alfarma ta miliyoyi (Hotuna)

Kyal-kyal-banza: Wani dan Najeriya ya bizne mahaifin sa cikin motar alfarma ta miliyoyi (Hotuna)

- Wani dan Najeriya ya jefa jama'a da dama cikin al'ajabi

- Dan Najeriyar dai ya binne mahaifin sa ne a cikin wata motar alfarma

- Motar da aka binne mahaifin dai ta zama kamar akwatin gawar ne

Akan ce daman 'yan Najeriya masu gudanar da abun mamaki a duniya. Nan ma dai wani abun al'ajabin ne ya faru a wani kauye dake a kudancin kasar inda muka samu labarin wani ya sayi sabuwar motar alfarma kirar BMW ya kuma binne mahaifin sa da ita.

Kyal-kyal-banza: Wani dan Najeriya ya bizne mahaifin sa cikin motar alfarma ta miliyoyi (Hotuna)
Kyal-kyal-banza: Wani dan Najeriya ya bizne mahaifin sa cikin motar alfarma ta miliyoyi (Hotuna)

KU KARANTA: Bam a bola ya tashi da yara 3 a Mubi

Mutumin dai an ce sunan sa Abubuike kuma dan asalin karamar hukumar Ihiala ne dake a jihar Anambra wanda lamarin ya jawo cece-kuce sosai musamman ma a kafafen sadarwar zamani.

Hotunan da suka rika yawo a kafafen sadarwar zamani dai sun nuna yadda al'ummar kauyen da dama suka halarci wurin binne mahaifin domin ganema idon su.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng