Alkalumma: Dalilin da yasa Mutane 80 suka kashe kansu cikin watanni 13 a Najeriya

Alkalumma: Dalilin da yasa Mutane 80 suka kashe kansu cikin watanni 13 a Najeriya

Bincike ya nuna kalla mutane 80 ne suka kashe kansu da kansu a Najeriya, cikin watanni goma sha uku, wanda hakan ke ayyana karuwar lamarin kashe kai a kasar kamar yadda wani rahoto na jaridar Daily Trust ta tabbatar.

Yawancin dalilan dake sa mutane kashe kansu baya wuce matsalar talauci, matsalolin aure, kalubalen karatu kamar yadda binciken ya nuna, wanda yace jihar Legas ce ta daya a yawan adadin mutanen da suka kashe kansu da suka kai mutum goma sha hudu,14.

KU KARANTA: Dakarun Sojin Najeriya sun yi ma masu garkuwa da mutane kisan kiyashi a Kaduna

Haka zalika wani bincike da hukumar lafiya ta majalisar dinkin Duniya, WHO, ta yi ya nuna mutane dubu dari takwas ne suke mutuwa duk shekara a duk fadin Duniya ta hanyar kashe kai, hakan na nufin mutum 1 na mutuwa a duk dakika 40. Matsalar tafi kamari a tsakanin yan shekaru 15-29.

Alkalumma: Dalilin da yasa Mutane 80 suka kansu cikin watanni 13 a Najeriya
Alkalumma

Rabe raben kasashen da suka fi samun matsalar kashe kai a tsakanin yan kasar sun bayyana Najeriya a matsayin kasa ta 10 a Duniya, Togo 26, Sierra Leone 11, Angola 19, Equatorial Guinea 7, Burkina Faso 22 da Cote d’Ivoire 5.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Likitoci sun bayyana cewa damuwa ne ke sanya mutane kashe kansu, inda wani likita dake Asibitin Aminu Kano, Mustapha Gudaji yace nakasa na sanya mutane burin kashe kansu, kamar yadda shaye shaye, halin bakin ciki, rashin aikin yi da sauransu ka iya sawa.

Dayake karin haske game da matsalar, wani Malamin addinin Musulunci, Ustaz Maisuna M Yahaya ya bayyana cewa haramun ne mutum ya kashe kansa a Musulunce, amma yace halin da matasa ke shiga na rashin aikin yi, rashin kudi, na kais u ga halaka. Haka zalika marayu, zawarawa da marasa galihu su kan yanke shawarar kashe kansu duba da matsanancin halin rashin kulawa da suka samun kansu a ciki.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel