Wani ɗalibi ya ɗebo ruwan dafa kansa, bayan satar wayar salula da kuma Kwamfuta
- Asirin wasu matasa ya tonu bayan da suka saci kayan wani
- Yanzu haka guda ya shiga hannu yayin da dayan kuma ya arce
- Mutukar ya gaza cika sharuddan belinsa akwai yiwuwar zai yi bikin Sallarsa a kurkuku
Wani ɗalibi mai suna Bawa Jeremiah ya gurfana gaban kuliya yau Litinin a Kaduna bisa zargin sibare salula da na'ura mai kwakwalwa.
Saurayin mai shekaru 20, mazaunin unguwar ƙauyen Gbangyi kuma an gurfanar da shi ne kan tuhuma biyu; sata da kuma haɗin baki.
Ɗan sanda mai gabatar da ƙara Sajan Luka Yilgi ya shaida wa kotun cewa, wani ɗalibi ne mai suna Joseph Ikechukwu ya kai ƙarar faruwar lamarin ga ofishin ƴan sanda na Sabon Gari ranar 30 ga watan Mayu.
Yilgi ya cigaba da bayyanawa kotun yadda Bawa da wani Umar Mohammed su kayi haɗin baki wajen haura gidan Joseph suka saci kwamfutarsa da wayar hannu da kuɗinsu ya kai N200, 000. Amma sai dai a lokacin da suke satar makocin Joseph ɗin ya gansu.
KU KARANTA: Wata fusatacciyar karuwa ta yayyagawa wani ‘dan sanda kaya sannan ta galla masa cizo
Bayanda ƴan sanda suka kai musu farmaki ne abokin satar tasa ruga da wayar da kuma kwamfutar, yayinda shi kuma Bawa ya shiga hannu.
A cewarsa wannan laifi ya saɓawa sashi na 271 da kuma na 302 na kudin shari'a jihar Kaduna.
Amma sai dai wanda ake ƙarar ya musanta aikata laifin da ake tuhumarsa da su.
Daga nan ne kuma alkalin kotun mai shari'a Ibrahim Sidi ya bayar da belinsa kan kuɗi Naira N50,000 da kuma waɗanda zasu tsaya masa mutum biyu, amma idan ba'a samu ba to sai a ingiza keyarsa zuwa gidan maza.
Kana ya ɗaga shari'ar zuwa ranar 18 ga wata domin cigaba da sauraren karar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng