Muje zuwa: Fashola yayi alƙawarin gyara Gadar Mowo da ta rufta nan da awa 72h
- Gwamnatin tarayya ta dauki matakin gaggawa don magance gyran wata gada da ta rufta
- Gadar dai ta rufta ne sakamakon ruwan sama kamar da bakin karya da aka maka
- Ministan ya kuma bawa masu amfani da titin hakuri musamman direbobin manyan Motoci
Ministan aiki Makamashi da Gidaje Babatunde Raji Fashola ya lashi takobin kammala gyaran gadar Mowo wadda ta haɗa titin Mokwa - jebba da fa zaftare ta burma a cikin awanni 72h.
Fashola ya tabbatar da hakan ne ga manema labarai a Zaria na jihar Kaduna jim kaɗan bayan ya kaiwa Mai martaba Sarkin Zazzau ziyarar bangirma Dr Shehu Idris a fadarsa jiya Lahadi.
Kafin dai ziyarar tasa Ministan ya halarci ƙaddamar da buɗe wata sabuwar na'urar rumbun wuta mai ƙarfin 60MVA/132/KV domin haɓaka samar da wutar lantar a birnin na Zaria da kewaye.
Ministan ya shaida cewa ma'aikatarsa ta tattaro ƙwararrun ma'aikata daga ma'aikatu da dama domin ganin an ɗauki matakin gaggawa na kawar da cinkoson ababen hawa a kan hanyar mararrabar Mowo da kuma kan titin Makwa zuwa Jebba kafin lokacin da za'a kammala gyaran gadar nan da awanni 72.
KU KARANTA: Harin kunar bakin wake cikin dare ya hallaka mutane 3 a Maiduguri
Fashola ya ɗora alhakin lalacewar gadar bisa mamakon ruwan sama da aka tafka kamar da bakin kwarya.
Masu ababen hawa sukan bi gadar musamman masu zuwa Abuja da Ilorin, kuma nisan gadar da jihar Niger ya kar kimanin kilomita 18.
Fashola ya ce "Mun san tabbas rugujewar gadar da kuma tsaikon gyaranta zai haifar rashin jin daɗi ga masu amfani da hanyar, amma muna rokonsu da suyi haƙuri domin idan abu makamancin haka ya faru dole sai an haɗa da haƙuri".
"Shekarar da ta gabata gadar Tatabu ma ta rufta a dalikin ruwan sama kuma mun kai ɗauki, wannan karon ma mun bayar da umarnin kawo kayan aiki domin magance matsalar". Ministan ya jaddada.
Sannan kuma ya ce ma'aikatarsa ta tuntuɓi shugabannin ƙungiyar direbobin manyan Motoci NUPENG don su shaidawa mambobins abinda ya faru da kuma ƙoƙarin da ma'aikatarsa take.
"Nan da awanni 72h na tabbatar zamu samu babbar nasarar dawo da gadar yadda masu ababen hawa zasu fara bi".
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng