‘Yan sanda sunyi ram da wasu gaggan masu garkuwa da mutane da suka goge wurin amfani da kakin jami’an tsaro

‘Yan sanda sunyi ram da wasu gaggan masu garkuwa da mutane da suka goge wurin amfani da kakin jami’an tsaro

- Rana ta kufcewa masu san'ar garkuwa da mutane

- Bayan da jami'an 'yan sanda suka gano maboyar aikata laifukansu

- Ba tare da wani artabu ko zub da jini ba, cikin salo na kwarewa da iya aiki, jami'an 'yan sandan suka musu kofara rago suka damke su

Jami'an ‘yan sandan sashin fiƙira karkashin ofishin babban Sufeton ‘yan sanda na kasa baki daya sun yi nasarar cafke wasu manyan masu garkuwa da mutane a jihar Legas. Wadanda suka shiga hannun ana zargin sun fito ne daga cikin kungiyoyin ‘yan ta'addan nan na ne da su kayi kaurin suna na yankin Ikotun da kewaye.

‘Yan sanda sunyi ram da wasu gaggan masu garkuwa da mutane da suka goge wurin amfani da kakin jami’an tsaro
‘Yan sanda sunyi ram da wasu gaggan masu garkuwa da mutane da suka goge wurin amfani da kakin jami’an tsaro

Jami'an tsaron sun dade suna fako tare sa ɗana tarko domin kama masu laifin, wanda suka kasance ko da yaushe suna yin shiga irin ta jami'an tsaro sannan su tare manyan tituna wanda ta hakan ne suke yin garkuwa da mutane.

Wata majiya ta shaida cewa jami’an tsaron sun bayyana cewa sun samu wasu bayanan sirri ne dake nuna cewa masu garkuwar zasu fito domin gunadar da aikinsu a daidai madakatar mota ta NNPC, wanda ta haka jami’an suka ɗana musu tarko.

KU KARANTA: An kama wani Fasto dumu-dumu yana yayyaga Qur’ani yana konawa a jihar Kogi (Hotuna)

Majiyar ta ce "Wannan masu laifin sun dade suna bamu matsala saboda suna yawo da motoci ne wanda suke dauke da lamba ta musamman don haka yasa jami'an yan sanda basa dakatar da su domin bincike".

"A lokacin da mutanen mu suka isa yankin sai muka gano wata mota kirar Lexus SUV wadda masu laifin suna ciki, amma jim kadan sai suka gane cewa jami'an tsaro na biye da su nan take suka fara gudu da motar tasu".

"Da yake dubun su ta cika suna cikin gudun ne sai motar tasu ta basu matsala yayin da ta makale a wani wuri, wanda a nan ne jami'an mu suka cim musu har suka samu nasarar damƙe su. Yanzu haka dai za a maida su can babban ofishin bincike domin suna da matukar haɗari barinsu a nan".

Kamara yadda majiyar ta bayyana.

Amma sai dai duk wani yunkuri da majiyarmu tayi don jin ta bakin Sufiritanda Chike Oti yayin rubuta wannan rahota ya ci tura

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng