Bakin kishi ya sa wani matashi a garin Potiskum yiwa budurwar sa yankan rago

Bakin kishi ya sa wani matashi a garin Potiskum yiwa budurwar sa yankan rago

- Bakin kishi ya sa wani matashi a garin Potiskum yiwa budurwar sa yankan rago

- Matashin ya ce ya aikata haka ne saboda iyayen budurwar sun ki amincewa ya aure ta

- Hukumar 'yan sandan jihar dai ya tabbatar da faruwar lamarin

Batun da ke iske mu na dauke ne da labarin wani matashi a garin Potiskum mai suna Muhammad Isa Adamu da tsananin kishi ya sanya ya hau dokin zuciyar sa ya yi wa budurwar sa mai suna Hauwa yankan rago.

Bakin kishi ya sa wani matashi a garin Potiskum yiwa budurwar sa yankan rago
Bakin kishi ya sa wani matashi a garin Potiskum yiwa budurwar sa yankan rago

KU KARANTA: Adam A. Zango ya siyawa mahaifiyar sa sabuwar mota

Kamar dai yadda muka samu daga majiyoyin mu, matashin ya bayyana cewa ya aikata wannan danyen aikin ne saboda iyayen budurwar sun ki amincewa ya zama mijin ta shi kuma ba wadda yake so kamar ta a duniya.

Legit.ng ta samu haka zalika daga bakin matashin cewa ya gayyaci budurwar ta sa ne ya zuwa wajen gari inda bayan sun gama zantawa sai kawai ya labbace ta ya daba mata wuka a wuyan ta.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar dai ya tabbatar da faruwar lamarin inda kuma ya ce suna kan bincike sosai kafin nan gaba su gurfanar da shi gaban kotu.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel