Ribar Ramadan: Kiristoci 36 ne suka karbi musulunci a wajen wa'azin Malam Daurawa

Ribar Ramadan: Kiristoci 36 ne suka karbi musulunci a wajen wa'azin Malam Daurawa

Wata kididdiga da aka gudanar tun daga farkon fara gabatar da wa'azin watan azumin Ramadana da fitaccen malamin addinin nan Sheikh Malam Ibrahim Daurawa yake yi an samu akalla mutane 36 da suka musulunta.

Mun samu dai cewa shahararren malamin yana gabatar da tafsirin Alqur'ani mai girma ne a masallacin Jekadafari a garin Gombe, babban birnin jihar ta Gombe da ke a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya.

Ribar Ramadan: Kiristoci 36 ne suka karbi musulunci a wajen wa'azin Malam Daurawa
Ribar Ramadan: Kiristoci 36 ne suka karbi musulunci a wajen wa'azin Malam Daurawa

KU KARANTA: Wani fasto ya musulunta a jihar Ebonyi (Bidiyo)

Legit.ng ta samu cewa shi dai Malam Daurawa shine shugaban hukumar Hisba ta jihar Kano kuma kamar yadda aka saba a bisa al'ada, kungiyar Izala ta kasa takan tura malamai ya zuwa garuruwa da dama domin gabatar da tafsiri a watan Ramadana.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a kwanan baya ma dai gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Ganduje shime ya jagoranci musuluntar wasu maguzawa da dama a masallacin gidan gwamnatin jihar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng