Mutum 1 ya rasa ransa, an cafke 2 a wani rikici da ya barke a kaduna

Mutum 1 ya rasa ransa, an cafke 2 a wani rikici da ya barke a kaduna

- Mazauna Unguwar shanu a jihar Kaduna sun fusknaci tashin hankali sakamakon wani kicibis mugun gamo da 'yan Sarasuka su kayi

- Rikicin dai ya mumunan matuka har ma yayi sandiyyar salwantar rai

- 'Yan sanda sun yi gaggawar kai dauki yankin har ma sun cika hannunsu

‘Yan sanda sun daka wawa ga wasun gungun ‘yan daba yayin da suka kashe Mutum 1 a wata arangama a Kaduna.

Mutum 1 ya rasa ransa, an cafke 2 a wani rikici da ya barke a kaduna
Mutum 1 ya rasa ransa, an cafke 2 a wani rikici da ya barke a kaduna

A jiya ne dai wani hautsini da tashin hankali ya faru a Unguwar Shanu dake yankin arewacin Kaduna inda ake zargin ko matasan da rikicin ya barke a tsakaninsu yan kungiyar nan ce ta Sarasuka ne.

Mai magana da yawun hukumar yan sanda ta jihar, ASP Muktar Aliyu, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyanawa manema labarai cewar mutum daya ya rasu sai dai ba a bayyana sunansa ba, kuma ya ce hakanya faru ne a dalilin rikicin da ya barke tsakanin matasan yankin Abakpa da na Anguwar Shanu.

KU KARANTA: Da sauran tsalle: ‘Yan sanda sun kara gano wata alaka mai karfi tsakanin ‘yan fashin Offa da Saraki

ASP Mukhtar ya dai bayyana cewa lamarin ya soma ne tun ranar Juma'a har zuwa jiya asabar inda ‘yan sandan suka samu kiraye-kiraye daga mutane da dama har hankalinmu yaje wajen, kuma ya ce sun kai sumame har ma sunyi nasarar cafke mutum biyu ragowar kuma sun arci ana kare.

Ya kara da cewa shugaban hukumar yan sandan jihar Austin Iwar, ya umarci iyayen yaran da manyan mutane da kuma duk wani mai fada aji a yankin da su zo a zauna domin nemo mafita tare da kawo karshen irin wannan rikici dake aukuwa a tsakanin matasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng