Dandalin Kannywood: Jarumi Adama A. Zango ya baiwa mahaifiyar sa kyautar tsaleliyar motar alfarma

Dandalin Kannywood: Jarumi Adama A. Zango ya baiwa mahaifiyar sa kyautar tsaleliyar motar alfarma

Tabbas, kamar da yadda addinin musulunci ya koyar da mu, dayan bautar Allah S.W.T da bin sunnar manzon sa, Annabi, S.A.W sai kyautatawa iyaye. Wannan kyautatawar kuwa ga iyaye ba ta da iyaka idan dai har ba ta sabwa Allah da manzon sa ba dai dai gwargwadon hali.

Haka ma dai tabbataccen al'amari ne cewar dukkan mai kokarin kyautatawa iyayenshi to ana kyautata ma sa zaton samun rayuwa mai albarka a duniya da lahira.

Dandalin Kannywood: Jarumi Adama A. Zango ya baiwa mahaifiyar sa kyautar tsaleliyar motar alfarma
Dandalin Kannywood: Jarumi Adama A. Zango ya baiwa mahaifiyar sa kyautar tsaleliyar motar alfarma

KU KARANTA: Ganawar Saraki da 'yan fim ta jawo sabon rikici a masana'antar

Legit.ng ta samu cewa a nan ma labari ne muka samu na cewa fitaccen tauraron fina-finan Hausa kuma Mawakin nan, Adam A. Zango ya farantawa mahaifiyarshi rai ta hanyar sai mata mota.

Shi dai jarumin Adamu ya saka faifan bidiyon a dandalinshi na sada zumunta inda aka nunashi lokacin da yake mikawa mahaifiyar tashi kyautar motar.

Har ila yau an kuma nuna jarumin lokacin da suke addu'a a tare.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel