Gwamnati za ta sake waiwayar batun kisan Bola Ige wanda Obasanjo ke da hannu a ciki

Gwamnati za ta sake waiwayar batun kisan Bola Ige wanda Obasanjo ke da hannu a ciki

Rahotanni sun kawo cewa wata majiya daga hukumar yan sanda ta nuna cewa gwamnati ta kammala duk wani shiri da ya kamata domin sake bude bincike akan kisan Tsohon ministan shari’a, Bola Ige.

Ana dai zargin tsohon shugaban ksa Olusegun Obasanjo da hannu a cikin kisan nasa wanda aka aiwatar a 2003.

Majiyar ta nuna cewa duk da yake a wancan lokacin kotu ta wanke wanda ake zargi da kisan, Iyiola Omisore amma doka ya bayar da dama na sake ci gaba da bincike kan laifin.

Haka ma, rundunar 'yan sandan za ta sake bude bincike kan kisan da aka yi wa jigon Tsohuwar jam'iyyar ANPP, Marshall Harry, a zamanin mulkin Obasanjo.

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya hana mashawarcinsa na musamman kan kafafen yadda labarai Femi Adesina mayar da martani ga wasikar tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo saboda ba sa'an sa bane.

KU KARANTA KUMA: Abunda na fadama su Ali Jita da sauran matasa da suka kawo mun ziyara – Shugaba Buhari

Shugaba Buhari ya yi wannan bayanin ne lokacin da ya ke karbar bakuncin kungiyar magoya bayansa a fadar Aso Villa da ke Abuja a daren jiya.

Buhari ya kuma ce dalili na biyu da ya sa bai mayar da martani kan wasikar ba shine saboda shi da Obasanjo dukkansu sojoji ne.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel