Kasuwa ta bude mun tunda Buhari ya kaddamar da June 12 – Mai siyar da jarida

Kasuwa ta bude mun tunda Buhari ya kaddamar da June 12 – Mai siyar da jarida

Ibrahim Usman, wani mai siyar da jarida a Gombe, yace kasuwa ta bude masa sosai tunda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da June 12 a matsayin ranar damokradiyyar Najeriya.

A ranar 6 ga watan Yuni, shugaba Buhari ya kaddamar da ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar damokradiyya inda zai maye gurbin 29 ga watan Mayu.

Shugaban kasar ya yanke wannan hukunci ne domin karrama marigayi Moshood Abiola, wanda ya lashe zaben shugaban kasa 12 ga watan Yuni 1993 a Najeriya.

Sai dai janar Ibrahim Babangida shugaban kasa a mulki soji na waccan lokacin yayi masa juyin mulki.

Kasuwa ta bude mun tunda Buhari ya kaddamar da June 12 – Mai siyar da jarida
Kasuwa ta bude mun tunda Buhari ya kaddamar da June 12 – Mai siyar da jarida

Usman ya sanar da kamfanin dillancin labarai na Gombe a ranar Juma’a cewa tunda aka kaddamar da wannan rana, mutane da daman a uwa siyan jarida domin karanta sharhin mutane daban-daban.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Babu hutu a ranar 12 ga wata Yuni – Gwamnatin tarayya

Yace hakan da shugaban kasar yayi ba karamin bajinta bane domin hakan ya sa ya zamo mai kishin damokradiyyar kasar.

Mai siyar da jaridan yace hatta da magauta sun yaba masa akan wannan karamcin da yayi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Domin samun ingantattun labarai ku bide mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng